<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Yesu Ya Cece Ni, Za Ya Taya Ni LW228</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu ya cece ni, za ya taya ni.
 Muddar ya riKe ni, tsoro ba na ji.
 Shi amintacce ne, sai in dogara,
 Duk alkawaransa za ya aikata.

[V2]
 2) Yesu ya same ni, huntu, ƃatacce.
 Ina so in ji shi, kullum shi kaɗai.
 Sa'ad da ya kira, amsa za mu yi,
 Ko'ina ya nufa sai mu riƙa bi.

[V3]
 3) Yesu Makiyayi, shi ya ba da rai
 Kada tumakinsa duk su lalace.
 Ubansa mai ƙauna yana riƙonmu,
 Daga hannuwansa ba mai fizgewa.

[V4]
 4) Yesu Makiyayi, shi ne ƙofar rai,
 Masu Bi sun shiga dukansu sosai.
 Sa'ad da zai komo, za ya tattara
 Dukanmu gabansa, ma ga fuskarsa.</lyrics>
<hymn_number>228</hymn_number>
</song>